Somaliya: Dubban Kananan Yara Suna Fuskantar Mutuwa Saboda Yunwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21770-somaliya_dubban_kananan_yara_suna_fuskantar_mutuwa_saboda_yunwa
Cibiyar kasa da kasa ta bada agaji ta ce da akwai kananan yara kusan 20,000 da su ke fuskantar mutuwa saboda yunwa a kasar Somaliya.
(last modified 2018-08-22T07:00:19+00:00 )
Jun 30, 2017 02:05 UTC
  • Somaliya: Dubban Kananan Yara Suna Fuskantar Mutuwa Saboda Yunwa

Cibiyar kasa da kasa ta bada agaji ta ce da akwai kananan yara kusan 20,000 da su ke fuskantar mutuwa saboda yunwa a kasar Somaliya.

Cibiyar kasa da kasa ta bada agaji ta ce da akwai kananan yara kusan 20,000 da su ke fuskantar mutuwa saboda yunwa a kasar Somaliya.

Shugaban kungiyar Hassan Nur Sa'id ya sanar a jiya alhamis cewa; rashin abinci mai gina jiki ne ya ke yin babbar barazana ga kananan yaran da kasarsu ta ke fama da fari.

Sa'adi ya kara da cewa; A bana ba sami saukar ruwan sama na azo a gani ba, don haka ba a sami amfanin gona ba, da hakan ake samun karuwar damuwa dagane da cimaka a wannan kasa.

Sa'adi ya kuma ce matukar ana son a magance matsalar yunwa a kasar ta Somaliya da hana mutane mutuwa saboda ita, to da akwai bukatar dalar Amurka biliyan daya da rabi, amma a yanzu abinda ake da shi a hannu shi ne dala miliyan 550.