Afrika Ta Tsakiya : Ana Cikin Mawuyacin Hali A Yankin Bria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21784-afrika_ta_tsakiya_ana_cikin_mawuyacin_hali_a_yankin_bria
Kungiyar likitoci marar iyaka ta (Médecins Sans Frontières/Doctors Without Borders ta ce halin da ake ciki a yankin Bria na Jamhuriya Afrika ta tsakiya na kara tabarbarewa.
(last modified 2018-08-22T07:00:19+00:00 )
Jun 30, 2017 05:53 UTC
  • Afrika Ta Tsakiya : Ana Cikin Mawuyacin Hali A Yankin Bria

Kungiyar likitoci marar iyaka ta (Médecins Sans Frontières/Doctors Without Borders ta ce halin da ake ciki a yankin Bria na Jamhuriya Afrika ta tsakiya na kara tabarbarewa.

A  mako guda da ya gabata dariruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wani kazamin rikici da ya hada gungun mayaka a yankin dake tsakiyar wannan kasa.

Kungiyar ta ce abubuwan jin kai da ake bukata na da yawa a wannan yakin, inda ake bukatar ruwan sha da wuraren tsugguni.

Kimanin  mutane dubu arba'in da bakwai ne ke cikin jiran wannan dauki cikin gaggawa a cewar Mumuza Muhindo wanda ke jagorancin aikin kungiyar ta MSF a wannan yakin tun cikin shekara 2016.