An Bukaci Ci Gaba Da Yaki Da Yunwa A Sudan Ta Kudu
Kungiyoyin Kai Agajin gagguwa na kasa da kasa sun bukaci da a ci gaba da kokari wajen yaki da rashin abinci a kasar Sudan ta kudu.
A cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan juma'a gamayar kungiyoyin kai agajin gaggauwa na kasa da kasa sun sake kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kara kokari wajen yaki da karamcin abinci gami da masifar yunwa da ta samo asali sanadiyar yaki da kuma fari a kasar Sudan ta Kudu.
Sanarwar ta ce har yanzu Al'ummar kasar Sudan ta kudu na cikin mawuyacin hali, musaman ma kananen yara da suke fama da rashin abinci mai gina jiki.
Daga farkon wannan shekara ta 2017 da muke ciki zuwa yanzu sama da kananen yara miliyan daya ne na kasar Sudan ta kudu suke fama da rashin lafiya sanadiyar karamcin abinci, ko baya ga hakan an bayyana cewa adadin kananen yaran da suke fama da cutar kanda ya karu a kasar.