An Hallaka Mayakan Al-shabab Shida A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21796-an_hallaka_mayakan_al_shabab_shida_a_somaliya
Dakarun Tsaron Somaliya sun hallaka mayakan kungiyar Ashabab 6 a kudancin kasar
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jun 30, 2017 13:43 UTC
  • An Hallaka Mayakan Al-shabab Shida A Somaliya

Dakarun Tsaron Somaliya sun hallaka mayakan kungiyar Ashabab 6 a kudancin kasar

Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Abdullahi Ali Anwad Babban Dakarun tsaron kasar Somaliya na cewa Mayakan kungiyar Ashabab sun hai farmaki barikin Sojojin kasar na yankin Shabul wusta dake kudancin kasar , a yayin fafatwar Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka mayakan Ashabab din guda shida tare da jikkata wasu da dama na daban daga cikinsu.

Anwad ya kara da cewa a bangaren Sojojin kasar Sun rasa Mutum guda, a farkon wannan maku ne Dakarun kasar suka bayyana shirisu na fara kai farmaki kan mayakan kungiyar Ashabab da nufin kakkabe su daga wannan yanki.

A 'yan kwanakin baya bayan nan mayakan Ashabab din sun tsananta kai hare-hare a kan Dakarun kasar ta Somaliya  da kuma Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka dake cikin kasar.