An Sami Baraka A Cikin Shuwabannin Kungiyar Al-Shabab Ta Somalia
Wasu labarai sun bayyana cewa kakakin kungiyar Al-shabab ta kasar Somalia ya balle daga kungiyar kuma a halin yanzu yana goyon bayan sulhuntawa da gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa kakakin kungiyar al-shaba Mukhtar Ruboo Abu-mansur wanda aka fi saninsa da Ruboo, wanda kuma ya kasance mataimakin shugaban kungiyar al-shaba na kasar somalia a halin yanzu ya balle daga babbar kungiyar kuma yana goyon bayan yayan kungiyar su sulhunta da gwamnatin kasar a kuma kawo karshen zubar da jina a kasar.
Reuters ta kara da cewa Mukhtar ya fara bayyana ra'ayinsa na sulhuntawa da gwamnati tun shekara ta 2013, amma hakan bai bayyana ba sai daga baya.
Har yanzun dai gwamnatin kasar Somalia bata bada labarin cewa Mukhtar ya mika kansa ga jami'an tsaron kasar ba. Kungiyar Al-shabab dai tana iko da wasu yankuna na kan iyaka da kasar Kenya a cikin kasar ta Somalia da kuma wasu kananan garuriwa a cikin kasar.