Shugaban Kasar Burundi Ya Bukaci Taimakon Kudi Na Gudanar Da Zaben 2020
(last modified Sun, 02 Jul 2017 06:32:09 GMT )
Jul 02, 2017 06:32 UTC
  • Shugaban Kasar Burundi Ya Bukaci Taimakon Kudi Na Gudanar Da Zaben 2020

Shugaban Kasar Burundi ya bukaci Taimakon kudi ga 'yan kasar domin gudanar da zaben Shugaban kasar a shekara 2020

A yayin da yake ishara kan halin tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma mahimancin gudanar da zaben Shugaba kasa a shekarar 2020, Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya bayyana cewa Gwamnati ba ta da kudiri neman taikmakon kudaden zaben daga kasashen waje ba, domin haka ya zama wajibi Al'ummar kasar su shiryawa saka hannu wajen tanadar da kudaden da za a gudanar da zabe da su.

Nkurunziza ya kara da cewa wasu daga cikin kasashen Duniya na farin ciki da mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ya shiga, domin haka idan aka bukaci taimakon kudi daga wajensu za su yiwa kasar illa.

Har ila yau Shugaban kasar Burundin ya sanar da buda wani Asusu a babban bankin kasar domin tattara kudaden gudanar da zaben.

A watan Avrilun 2015 ne, kasar Burundin ta fada cikin rikcin siyasa, bayan da Shugaba Nkurunziza ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar Shugabacin kasar a karo na uku, lamarin da 'yan adawa ke ganin cewa ya sabawa kundin tsarin milkin kasar.