Rikici A Afirka Ta Tsakiya Ya Kashe Mutum 15
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21866-rikici_a_afirka_ta_tsakiya_ya_kashe_mutum_15
Rahotanni daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na cewa a kalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu a wata musayar wuta tsakanin wasu gungun mayaka biyu a birnin Kaga-Bandoro dake tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:20+00:00 )
Jul 03, 2017 01:14 UTC
  • Rikici A Afirka Ta Tsakiya Ya Kashe Mutum 15

Rahotanni daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na cewa a kalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu a wata musayar wuta tsakanin wasu gungun mayaka biyu a birnin Kaga-Bandoro dake tsakiyar kasar.

Rikicin dai ya hada tsaffin mayakan Seleka da kuma dakarun tawagar Minusca ta MDD  a kasar a cewar wasu majiyoyi daga kungiyoyin agaji.

Wani jami'in wata kungiyar agaji ya shaida wa kamfanin dillancin labaren faransa na AFP cewa mayaka 15 ne suka rasa rasyukansu a musayar wutar.

Majiyoyin tsaro dai sun ce tsaffin mayakan na Seleka su ne ummul aba'isin hadassa hargitsin, inda kuma nan ne suka cio karo da dakarun Pakistan da na Burundi dake cikin tawagar ta Minusca.

Tawagar ta Minusca ta bakin kakakinta Vladimir Monteiro ta ce dakarunta sun cika aikinsu na kare al'aumma yankin da dukiyoyinsu.

Sai dai a nasu bangare mayakan na MPC da kamfanin dillancin labaren na AFP ya tuntubi kakakinsu nasu Aboulkassim Algoni Tidjani, ya ki ya ce uffan.