Onaiyekan: Ba Wanda Yake Da Shirin Musuluntar Da Nigeria
John Cardinal Anaiyekan, kuma Archbishop a cocin Catholica a Abuja, ya bayyana cewa ba wanda yake da wani shirin na maida dukkan yan Nigeria kiristoci, kamar yadda wasu kiristocin suke kokawa.
Jarisar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto Cadinal Onaiyekan yana fadar haka ne a Abuja a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa "kada wani ya yaudare ka, ya ce wai musulmi suna sun tilastawa kiristoci zama musulmi, amma idan sun yi haka ma suna da damar yin haka, matukar kai ma an baka damar ka kai sakon kirista ga dukkan musulman Nigeria idan zaka iya.
Onaiyekan, ya kammala da cewa, korafe-korafe ba zasu yi amfani ba, dole ne mu ta shi mu kai sakon yesu kiristi a ko ina a Nigeria. Matukar ba a shirye muke mu isar da sakon yesu ba, to kuwa muna cikin barazanar rasa imaninmu. Sannan matukar bamu yi kokarin yada kiristanci ba, to bamu cancanci zama kirista na gaskiya ba.