An Rarraba NNPC Zuwa Kamfanoni Guda 7
Mar 09, 2016 09:14 UTC
Minstan mai na kasa a Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu, ya fitar da wata sanarwa da ke cewa an raba kamfanin main a kasa NNPC zuwa kamfanoni guda 7.
Ya ce kamfanonin sun hada da kamfanin kula da rijiyoyin hakar mai, kamfanin binciken wuraren da ake sa ra samun danyen mai, kamfanin kasuwanci, kamfanin kula da matatun mai, kamfanin kula da iskar gas da lantarki, kamfanin kula da rijiyoyin main a cikin teku, kamfanin kula da tsare-tsaren ayyuka da kudaden na kamfanonin.
Kachikwu ya ce bayan sun kamala dukaknin tsare-tsarensu, sun mikawa shugaba Buhari, inda shi kuma bayan yin dubi kan hakan ya amince, wanda hakan ya mayar da wannan shiri nasu tabbataccea hukumance.
Tags