Jul 04, 2017 12:25 UTC

A jiya Litinin Allah ya yi wa Alh Dr. Yusuf Maitama Sule dan masanin Kano rasuwa a birnin Alkahira na Masar.

Alh Yusuf Maitama Sule dai fitaccen dan siyasa ne wanda ya taka rawa a dukaknin bangarori a Najeriya. Ya kasance cikin wadanda a ke damawa da su tun kafin kasar ta samu 'yancin kai daga mulkin mallaka na turawan Birtaniya, haka nan kuma bayan ta samu 'yancin kasa yana daga cikin mutane na farko daga arewacin Najeriya da suka taka rawa a bangarori daban-daban na ci gaban kasar.

An dai haifi marigayi Dr. Maitama Sule ne a jihar Kano kimanin shekara 88 da suka wuce, wanda kuma shahararren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya taba rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya zama minista lokacin Firai Ministan Najeriya na farko Alhaji Sir. Abubakar Tafawa Balewa, a shekarar 1976 ne aka ba shi kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da korafe-korafen jama'a, yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NPN wanda bai yi nasara ba, inda Alh. Shehu Shagari ya lashe zaben wanann shekara  a karkashin jam'aiyar tasu ta NPN, amma kuma gwamnatin ta Shehu shagari ta nada shi a matsayinjakadan tarayyar Najeriya a UN, inda UN ma ya kasance daya daga cikin shugabannin muhimmman kwamitoci na majalisar, wato kwamitin yaki da wariyar launin fata, wanda daya ne daga cikin muhimamn matsalolin da ake fama da su a wancan lokacin a wasu kasashen duniya.

Bayan nan kuma a shekara ta 1983 bayan kwashe shekaru hudu jam'iyyar NPN tana mulki a Najeriya, an sake gudanar da zabe, wanda Alh. Shehu Shagari ya sake lashewa a karkashin jam'iyyar ta NPN, daga nan kuma sai gwamnatin shagari ta ba shi mukamin minista mai kula da yadda ake tafiyar da kasa, inda ya ci gaba da rike wannan mukami har zuwa lokacin da Major Janar Muhammad Buhari ya jagoranci juyin mulki wanda ya kifar da gwamnatin NPN a lokacin, a karshen Disamban 1983.

Marigayi Dr, Yusuf Mai tamma Sule ya kasance mutum ne mai son jama'a da kuma hankoron ganin an zauna lafiya a tsakanin dukkanin al'ummar Najeriya, duk kuwa da bambancin Kabilu da addinai da al'adun da ke tsakaninsu, wanda hakan ne ya sanya yake da matsayin na musamman da dukaknin al'ummomin Najeriya suke girmama shi, duk kuwa da cewa shi ya fito ne daga arewacin kasar.

Marigayin ya bar matarsa guda da kuma 'ya'ya 10 maza 4 da kuma mata 6 da jikoki masu tarin yawa.

 

To dangane da wanann rashi da al'ummar Najeriya suka yi na daya daga cikin manyan dattijan kasar Dr Yusuf Mai tama Sule, mun ji ta bakin tsohon abokinsa tun daga lokacin kuruciya, shi kuma tsohon dan siyasa a Najeriya Alh. Tanko Yakasai.

 

 

Tags