An Fara Kamfe Na Neman A Kifar Da Gwamnatin Sisi A Masar
'Yan adawar siyasar kasar Masar da dama ne da suke rayuwa a wajen kasar suka kaddamar da wani kamfe da ke yin kira zuwa ga kifar da gwamnatin Abdulfattah Sisi .
Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da aka cika shekaru 4 da juyin mulkin da Sisi ya yi wa tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Morsi, wasu 'yan adawar siyasar kasar ta Masar da ke rayuwa a waje da adadinsu ya kai 934, sun sanya hannu kan wani sabon kamfe da ke yin kira da a kifar da gwamnatin Abdulfattah Sisi da suke kira gwamnatin kama karya.
Sisi dai ya fara fuskantar babban kalu bale daga al'ummar kasar masar ne sakamakon abin da suka kira gazawar gwamnatinsa ta fuskokin tsaro da tattalin arziki, da kuma yina mfani da karfin bindiga akan masu sabani da shi na siyasa.
Baya ga hakan kuma cefanar da tsibiran kasar guda biyu da ya yi ga masarautar iyalan gidan Saud da ke rike da madafun iko a Saudiyya, ya kara jawo masa bakin jini da adawa a tsakanin al'ummar kasar Masar.