Afirka Ta Kudu : Gobara Ta Kashe Mutane 7 A Johannesburg
Rahotanni daga birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu na cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sanadin wata gobara data kama wani bene.
Shida daga cikin mutanen sun mutu ne sanadin shakkar hayakin gobara, yayin da gudan ya mutu bayan ya duro daga saman benin don kaucewa gobarar.
Bayanai dai sun ce mutanen na rayuwa cikin benin ne ba bisa ka'ida ba.
Majiyoyin jami'an agaji sun ce wutar ta tashi a cikin ginin ne wanda babu wutar lantarki da ruwa a ciki da safiyar yau Laraba.
An yi nasara ceto mutane kimanin hamsin daga cikin banin yayinda wasu bakwai na daban suke kwance a asibiti.
Babu dai wani karin bayyani dangane da musababin tashin gobarar, saidai wasu ganau sun shaidawa kafofin yada labarai cewa, wani injin jenereto da wani mazaunin benin ke amfani da shiya hadassa gobarar.