Tanzaniya : An Kama 'Yar Majalisa Saboda Batanciwa Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21942-tanzaniya_an_kama_'yar_majalisa_saboda_batanciwa_shugaban_kasa
A Tanzaniya, an kama wata 'yar majalisa dokoki ta bangaren adawa saboda firta kalamen da ake alakantawa dana batanci ga shugaban kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:20+00:00 )
Jul 05, 2017 11:43 UTC
  • Tanzaniya : An Kama 'Yar Majalisa Saboda Batanciwa Shugaban Kasa

A Tanzaniya, an kama wata 'yar majalisa dokoki ta bangaren adawa saboda firta kalamen da ake alakantawa dana batanci ga shugaban kasar.

'Yar shekaru 39,  Halima Mdee sannanniya ce a kasar akan furta kalamen gaskia, saidai an zarge ta da firta wasu kalamai na cin fuskawa shugaban kasar John Magufuli.

Madame Halima ta bayyana a wani taron manema labarai a ranar Litini data gabata cewa, wasu kalamai dake sukan matakin shugaban kasar game da matsayinsa na cewa a kori duk 'yar wata yarinya data dauki a ciki daga makarantun gwamnati.

Saidai labarai bai bayyana takamaimai ba irin batancin da ake zargin 'yar majalisar ta yi wa shugaban kasar.

Wani dan majalisa na jam'iyyar adawa ta kasar mai suna Said Kubenea ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa ba'a gurfanar da 'yar majalisar ba gaban kuliya, aman ana sa ran gurfanar da ita gaban kotu a gobe Alhamis.

'Yan adawa a ksar dai na ganin wannan duk wani yunkuri na hana 'yan adawa tofa albarkacin bakinsu akan duk wani abu da ya shafi shugaban kasar.