An Kashe Sojojin Nijar Biyar A Iyaka Da Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21944-an_kashe_sojojin_nijar_biyar_a_iyaka_da_mali
Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na cewa sojojin kasar a kalla biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da wau ‘yan bindiga suka kai masu a kauyen Midal dake yammacin garin Tasara dake jihar Tawa a kusa da iyaka da kasar Mali.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 05, 2017 17:29 UTC
  • An Kashe Sojojin Nijar Biyar A Iyaka Da Mali

Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na cewa sojojin kasar a kalla biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da wau ‘yan bindiga suka kai masu a kauyen Midal dake yammacin garin Tasara dake jihar Tawa a kusa da iyaka da kasar Mali.

Harin dai an kai shi ne da sanyin safiyar yau Laraba kan tawagar sojojin dake yaki da safara miyagun kwayoyo.

Bayanai daga kasar sun ce maharan sun zo ne cikin motoci da kuma kan Babura inda suka kasha sojoji biyar da kuma raunana wasu uku.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da hukumomin kasar suka sanar da cewa an shiga biyar sahun mayakan nan da ake zargin cewa ‘yan boko haram da suka yi garkuwa da wasu mutane a yankin Diffa a ranar Lahadi data gabata.

Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar a yau, ta ce mutane 37 ne da suka hada da mata 26 da kuma maza 11 mayakan suka sace a kauyen Ngalewa dake jihar ta Diffa.