Wani Sabon Rikici Ya Hallaka Mutane 12 A Kasar D/Congo
Wani Sabon Rikici da ya barke tsakanin 'yan tawaye da Sojojin jamhuriyar D/Congo a jihar Kivo ta arewa dake gabashin kasar yayi sanadiyar mutuwar mutane 12
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto Kanal Dyodone Caserka kakakin Sojin jamhuriyar D/Congo a jiya Laraba na cewa a yayin musayar wuta tsakanin 'yan tawayen Mai-Mai da Sojojin kasar, Sojoji biyu ne suka rasa rayukansu yayin da aka kashe 'yan tawayen guda 9 sannan kuma wani farar hula guda shi ma ya rasa ransa.
Kanar Dyodone Caserka ya ce wani adadi na wucin gadi ne, akwai yiyuwar adadin ya karu saboda akwai mutane da dama da suka ji rauni kuwa wasu daga cikin su na cikin mawuyacin hali.
Kakakin Sojojin Congo na jihar Kivo ta arewa ya tabbatar da cewa Dakarun tsaron kasar sun tunkari tungar karshe na 'yan tawayen na Mai-Mai tare da cabke mayakan 'yan tawayen 4 da kuma wasu manyan makaman yanki na 'yan tawayen.
Cikin kwanaki biyun da suka gabata ana tabka kazamin fada tsakanin Dakarun tsaron jamhuriyar Demokariyar Congo da 'yan tawayen Mai-Mai a gabashin kasar.