An Hallaka Mayakan Ashabab Da Dama A Kudancin Somaliya
Dakarun Tsaron Somaliya Sun kai hari kan sansanin 'yan ta'addar Ashabab tare da hallaka 13 daga cikin su a kudancin kasar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba Ahmed Abdulahi Isse daya daga cikin manyan jami'an tsaron Somaliya ya ce Sojojin kasar sun kai wani farmaki kan wani sansanin koyar da aikin Soja na 'yan ta'addar Ashabab dake da nisan kilomita 25 da garin Kismayo a yankin Jubaland, inda suka hallaka 'yan ta'addar 13 tare da jikkata wasu da dama na daban daga cikin su.
Kismayo shi ne wurin tattalin arzikin karshe na mayakan kungiyar Ashabab, a shekarar 2012 Dakarun tsaron kasar tare da hadin gwiwar Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka Amison sun fatattaki mayakan na Ashabab daga wannan yanki.
Kungiyar Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar ta'addancin nan ta AlQa'ida an kafa ne a shekarar 2006 kuma shekaru biyar da suka gabata aka yi waje da su daga Magadushu babban birnin kasar Somaliya.kuma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a kasar.