Taron Kolin Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Karo na 26
Rikicin kasar Burindi da Yaki da ta'adanci ne yafi daukan hankali a taron na bana
A Ranar Asabar din nan aka bude babban taron shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 26 a cibiyarta dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Shugabannin kasashe mambobin kungiyar 54 ke hallartar taron na yini biyu karkashin taken ''2016: shekarar Afrika ta hakkin bil adama musamman a kan 'yan cin mata".
Sai dai batutuwan da suka fi mamaye taron sun hada da rikicin siyasar kasar Burundi musamen kan batun tura dakarun sulhu na kungiyar AU a Burundi wanda gwamnatin kasar taki amuncewa dashi.
A jawabin sa gun bude taron babban sakatare na MDD Ban ki Moon ya jaddada goyan bayan sa domin ganin an tura dakarun na wanzarda zamen lafiya a kasar ta Burundi dake fama da rikicin siyasa.
Mr Ban ki Moon ya ce yana goyan bayan tura masu sa ido na kungiyoyin kare hakin bil adama dama tawagar wazarda zamen lafiya domin kare a'umma da dukiyoyin su a wannan kasa.
A watan Disamba bara kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar tarraya Afirka ya amunce da kudirin tura dakaru 5,000 a Burindi akan fargabar da ake da ita na ci gaba da rikici a wannan kasa data taba fuskantar yakin basasa da yayi sanadin mutuwar mutane (300.000) a tsakanin shekara 1993 da 2006.
A gameda wannan batu dai gwamnatin Burindi ta bakin ministan harkokin wajen ta Alain Aimé Nyamitwe ta ce bata bukatar sojojin na kungiyar AU, koda yake rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar ci gaba da tattaunawa kan batun da shugabannin kasashen Afrika su ke yi a ranar karshe na taron da suke yi a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.
Alkaluma sun nuna cewa sama da mutane 400 ne suka rasa rayukan su a rikicin, yayin da wasu 230.000 ke gudun hijira a kasashe makofta domin tsira da rayukan su.
A hannu daya kuma taron na bana ya dauko batun yaki da ta'adanci dake zama babban kalubale ga kasashen nahiyar.
Taron na karo 26 ya kuma zabi Idris Deby Itmo shugaban kasar Chadi a matsayin shugaban karba-karba na kungiyar wanda ya maye gurbin shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabuye.
Shugaba Idriss Deby na daya daga cikin shugabanin Afirka na kudu da hamadar sahara da suka sanya kafar wando guda da kungiyar Boko Haram.
Idriss Deby dan shekaru 64 a duniya, ya kama mulkin kasar Chadi da sinin bindiga bayan hambarar da mulkin Hissen Habre a shekara 1990, bayan hakan ya dora kasar kan tafarkin demokuradiyya, hakan kuma ya bashi damar sayawa takara ya kuma lashe zaben shugabancin kasar na shekara 1996, koda yake 'yan adawa a kasar na masa zargin tafaka mugudi a zabubukan kasar, da toye hakkin bil adama, kuma duk da cewa kasar ta shiga jerin kasashe masu samar da man fetur akwai talauci daya yi wa al'ummar kasar katutu.
Chadi dai ta jima tana taimakawa a yake-yake da ake yi a yammacin Afirka inda ko a shekara 2013 ta taimaka da sojojin ta a yakin da masu kaifin kishin islama a yammacin kasar Mali, baya ga hakan kuma dakarun kasar na a sahun gaba a yakin da ake yanzu da kungiyar boko Haram ta Najeriya dake barazana ga kasashen makofta irin su Kamaru, Nijer, sanan iata da kan ta Chadi ta sha fuskantar hare-haren tsagerun.