Masar Ta Kori Daliban Indosiya 4
(last modified Sat, 08 Jul 2017 11:55:56 GMT )
Jul 08, 2017 11:55 UTC
  • Masar Ta Kori Daliban Indosiya 4

Masar Ta fitar da daliban jami'ar nan guda 4 'yan kasar Indanosiya da ta zarga da kokarin tayar da hankali

A wata sanarwa da ya fitar a wannan Assabar, Jakadan kasar Indanosiya dake birnin Alkahira ya tabbatar da cewa Daliban kasar sa da jami'an tsaron kasar Masar suka kame a watan jiya an mayar da su gida a yau din nan.

A ranar 6 ga watan yunin da ya gabata ne jami'an tsaron kasar Masar suka cabke wasu daliban jami'a 'yan kasar Indanosiya  dake karatu a cikin kasar guda 4,bayan da aka bayyana su a matsayin hadari na tsaron kasar.

Ofishin Jakadancin Indanosiya a birnin Alkahira ya ce har yanzu Gwamnatin Masar ba ta basu dalilan da ya sanya ta kama daliban kasar dake da izinin takardun zama a cikin kasar ba.

Kafin hakan dai, Hamli Fauzi jakadan indonesia dake birnin Alkahira ya yi watsi da zarkin da magabatan kasar Masar din suka yiwa daliban.