An Tarwatsa Zanga-zangar 'Yan Adawa A Madagaska
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22022-an_tarwatsa_zanga_zangar_'yan_adawa_a_madagaska
Jami'an tsaro a Madagaska sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa zanga-zangar 'yan adawa a Anatananarivo babban birnin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jul 08, 2017 13:01 UTC
  • An Tarwatsa Zanga-zangar 'Yan Adawa A Madagaska

Jami'an tsaro a Madagaska sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa zanga-zangar 'yan adawa a Anatananarivo babban birnin kasar.

'Yan adawa dai sun fito zanga zangar ce bisa kiran babbar jam'iyyarsu (TIM) ta tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana, domin murnarsu kan zagayowar shekaru 15 na jam'iyyar.

Tun da farko dama hukumomin kasar sun  haramta zanga-zangar inda suka jibge jami'an tsaro na yan sanda da Jandarmu da kuma sojoji a gaban filin wasan kwallon kafa na domin hana masu zanga-zangar shiga a ciki.

A cewar kwamandan jami'an jandarma na Antananarivo, Janar Njatoa-risoa Andrian-janaka basu cafke kowa ba daga cikin masu zanga-zangar, kana ba'a samu wani wanda ya jikkata ba.

Rikicin siyasa a wannan kasa mafi talauci a duniya na kara zazzafa a makwanin baya bayan nan, inda masu adawa da shugaban kasar ke zarginsa da matsin lambawa kotun kasar kan wata mashawarciya ta kusa da shi da ake zargi da karkata akalar wasu kudade.

Le climat politique s'est tendu ces dernières semaines sur la Grande île. Les adversaires du chef de l'Etat l'accusent d'avoir fait pression sur la justice au profit d'une de ses proches conseillères, incarcérée pour détournements de fonds.