Somaliya Tayi Hasarar Milyoyin Daloli Sakamakon Yankewar Internet
Yankewar sadarwar yanar Gizo yayi sanadiyar hasarar sama da miliyan dari na dalar Amurka ga tattalin arzikin kasar Somaliya
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Gwamnatin kasar Somaliya ta bayyana cewa yawan yankewar sadarwar yanar gizo cikin makunni biyu a kasar yayi sanadiyar hasarar milyan goma na $ a ko wace rana.
Ministan sadarwar kasar Abdi Anshor Hasan ya ce daga lokacin da aka fara yanke sadarwar yanar gizo zuwa yanzu kasar ta yi hasarar milyon 130 a bangaren tattalin arzikin kasar, ko baya ga hakan, yankewar Internet din ya janyo fishin Al'ummar kasar kuma yayi tasiri sosai a tsakiya da kudancin kasar daga ciki har da Magadushu babban birnin kasar.
Kasar Somaliya dai na daga cikin kasashen 4 da MDD ta bayyana su a matsayin masu fama da karamcin abinci sakamakon fari da kuma yaki, kasashen ukun sun hada da Yemen, Sudan ta kudu da Najeriya.