Mutane 9 Sun Hallaka Sanadiyar Harin Ta'addancin Ashabab A Kenya
(last modified Sun, 09 Jul 2017 11:12:45 GMT )
Jul 09, 2017 11:12 UTC
  • Mutane 9 Sun Hallaka Sanadiyar Harin Ta'addancin Ashabab A Kenya

Majiyar Tsaron Kenya ta sanar da mutuwar fararen hula 9 sakamakon harin ta'addanci na mayakan Ashabab kusa da kan iyakar kasar da Somaliya

Kafar watsa labaran Afirka time ta habarta cewa a yayin kai harin, maharan dake da alaka da kungiyar ta'addancin ta Ashabab sun kashe fararen hula 9 tare da jikkata wasu a kauyukan dake kan iyakokin kasashen Kenya da Somaliya.

Tuni dai Jami'an tsaro da na 'yan sanda suka fara gudanar da bincike domin gano wadanda aka kashen da kuma yadda aka kai harin.

Kafin hakan dai akwai labarin dake yado a kasar Kenya dake cewa akwai 'yan ta'adda 11 da suka samu horo na musamman daga kungiyar Ashabab da kuma suka shigo cikin kasar, lamarin da ya sanya karfafa matakan tsaro a fadin kasar gaba daya.

Har yanzu dai kungiyar ta Ashabab na rike da wasu yankuna a kasar ta Somaliya kuma ta kasance babbar barazana ga tsaron kasashen dake makwabtaka da kasar, ciki kuwa har da kasar Kenya.