An Hallaka Mayakan Ashabab Da Dama A Yammacin Somaliya
Akalalla 'yan ta'adda Ashabab 18 suka hallaka a yayin wani farmakin da Sojojin Somaliya suka kai arewacin kasar
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Kanar Muhamad Ismael daya daga cikin manyan jami'an tsaron Somaliya a wannan Litinin na cewa Dakarun tsaron kasar sun kai farmaki a maboyar 'yan ta'addar Ashabab a yankin Belad Bant dake arewacin kasar,tare hallaka 18 daga cikin su.
Ko baya ga hakan jami'in ya ce Sojojin kasar sun rusa maboyar 'yan ta'addar Ashabab da dama a yankin.
A nata bangare, kungiyar Ashabab ta tabbatar da kai harin, to saidai tayi watsi da kisan da Sojojin kasar suka ce sun yiwa mayakan nasu.
Duk da irin nasarorin da Sojojin kasar Somaliya tare da hadin gwiwar Dakarun wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka suka samu a kan kungiyar ta Ashabab, to amma har yanzu kungiyar dake da alakar kut da kut da kungiyar AlQa'ida na rike da wasu yankuna na kudancin kasar.