Tawagar Majalisar Dokokin Jamhuiryar Nijar Na Ziyara A Iran
Shugaban kwamitin kawance a tsakanin majalisun Iran da Nijar ya ce; Aiki tare a tsakanin kasashen musulmi zai sa su yin tasiri a fagen siyasar kasa da kasa.
Shugaban kwamitin kawance a tsakanin majalisun Iran da Nijar ya ce; Aiki tare a tsakanin kasashen musulmi zai sa su yin tasiri a fagen siyasar kasa da kasa.
Mahdi Farshad wanda ya gana da takwarana daga bangaren kasar jamhuriyar Nijar, Massani Cornei a nan Tehran a yau litinin ya yi ishara da yadda alakar kasashen biyu ta cika shekaru 30 sannan kuma ya kara da cewa: Kwamitin kawance na kasashen biyu a shirye ya ke domin shafe fagen yin aiki a tsakanin majalisun biyu.
Har ila yau Farshad ya ce kasar Iran za ta yi aiki a tare da Nijar a bangarorin tattalin arziki da kiwon lafiya da kasuwanci.
A nashi gefen, Massani Cornei daga Jamhuriyar Nijar, ya yaba da jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ya ce tana da matsayi a siyasar waje ta kasarsa.