An Sace Ma'aikatan UNICEF A Sudan Ta Kudu
An sace wasu daga cikin ma'aikatan asusun tallafa wa kananan yara na majlaisar dinkin duniya UNICEF a kasar Sudan ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ma'aikata uku ne na UNICEF a ka sace a kasar Sudan ta kudu kamar yadda hukumar ta sanar jiya, kuma dukkaninsu suna aiki ne tare da wata cibiya da ke da ahadin gwiwa da UNICEF da ke gudanar da ayyukan taimaka ma kananan yara a Sudan ta kudu ta fuskar ilimi.
Bayanin ya ce an sace mutanen ne biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin dakarun gwamnati da kuam wasu masu dauke da makamai.
Kwanakin baya ne hukumar UNICEF ta fitar da rahoto da ke cewa, kimanin kananan yara dubu 16 ne aka tilasta wa shiga aikin soji a kasar Sudan ta kudu, wanda hakan ya yi hannun riga da dokoki na majalisar dinkin duniya.