'Yan Adawa Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Zimbabwe
(last modified Thu, 13 Jul 2017 13:10:49 GMT )
Jul 13, 2017 13:10 UTC
  • 'Yan Adawa Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Zimbabwe

Magoya bayan jam'iyyun siyasa masu adawa da gwamnatin shugaban kasar Zimbawe Robert Mogabe sun gudanar da zanga-zanga a birnin Harare fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Associateec Press ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar sun bukaci shugaba Robert Mogabe da ya yi murabus daga shugabancin kasar, tare da zargin hukumar zaben kasar da yin magudi, wanda ya ba shi damar zarcewa kan mulki.

Rahoton ya ce jami'an 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsuhuwa da kuam fesa ruwa ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Ana guganar da wannan zanga-zanga ne a daidai lokacin da shugaba Mogabe dan shekaru 93 yake kwancea  asibiti a  kasar Singapore yana jinya.