Gambiya : An Kafa Kwamitin da Zai Binciki Kaddarorin Jammeh
(last modified Fri, 14 Jul 2017 16:07:03 GMT )
Jul 14, 2017 16:07 UTC
  • Gambiya : An Kafa Kwamitin da Zai Binciki Kaddarorin Jammeh

Shugaban Gambiya, Adama Barrow ya kafa kwamitin da zai binciki dukiyar da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya mallaka.

An dai dorawa kwamitin yaunin bincikar yadda Jammeh ya tafiyar da wasu ma'aikatu da dukiyar da ya mallak da kuma harkokin tafiyar da kudadensa da kuma na wasu mukarabansa.

Kwamitin dai na da wa'addin watanni uku domin gudanar da binciken da kuma bada sakamakonsa ga shugaban kasar Adama Barrow.

A watan Mayu da ya gabata ne ministan shari'a na kasar, Abubakar Tambadu, ya sanar da toshe dukiyar da Mista Jammeh ya mallaka, bayan zargin da hukumomin kasar sukayi masa na karkata wasu kudade da yawansu ya kai Dala Miliyan hamsin.

Mista Jammeh wanda ya mulki Gambiya na tsawan shekara 22 ya fice daga kasar ne a watan Janairu na wannan shekara inda yake zamen mafaka a kasar Equatorial Guinea.