Paul Kagame: Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa Da Za A Gudanar
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya bayyana cewa shi ne zai lashe zaben shugaban kasar da za a gudanar a kasar A cikin watan Agusta mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, Shugaba Paul Kagame ya bayyana sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'ar kasar kan gyaran kundin tsari mulki da cewa wata babbar ishara ce a kan cewa babu tantama shi ne shi ne zai lashe zaben da za a gudanar a kasar.
A cikin shekara ta 2015 ce aka gudanar da zaben raba gardama kan yin wa kundin tsarin mulkin kasar Rwanda kwaskwarima, domin bayar da dama ga Kagame ya zarce kan mulki, inda mafi yawan wadanda suka kada kuri'ar suka amince da gyaran kundin tsarin mulkin, wanda hakan ya bai wa Kamagame damar ci gaba da tsayawa takara har zuwa shekara ta 2034.
Tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar Rwanda a 1994, Paul Kagame yake a kan kujerar shugabancin kasar Rwanda.