Tattalin Arzikin Zimbabwe Na Kara Tabarbarewa, in ji IMF
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2224-tattalin_arzikin_zimbabwe_na_kara_tabarbarewa_in_ji_imf
Asusun ba da lamuni na kasa da kasa wato IMF ya yi kira ga mahukuntan kasar Zimbabwe da su gaggauta bullo da wasu dabaru masu kwari don farfado da tattalin arzikin kasar da ke kara shiga cikin mawuyacin hali.
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 10, 2016 03:10 UTC
  • Tattalin Arzikin Zimbabwe Na Kara Tabarbarewa, in ji IMF

Asusun ba da lamuni na kasa da kasa wato IMF ya yi kira ga mahukuntan kasar Zimbabwe da su gaggauta bullo da wasu dabaru masu kwari don farfado da tattalin arzikin kasar da ke kara shiga cikin mawuyacin hali.

Shugaban tawagar asusun na IMF Dominico Fanizza wanda ya bayyana hakan a wannnan Laraba a lokacin daya ziyarci kasar, ya ce, duk da cewa, kasar Zimbabwe ta cimma mizanin manufofi da gyare-gyarenta na harkokin kudi, amma tattalin arzikin kasar ya tabarbare sakamakon matsalar fari da karuwar darajar dalar Amurka idan aka kwatanta da kudin kasar Afirka ta kudu, babbar abokiyar cinikayyar kasar ta Zimbabwe.

Don haka jami'in ya yi kira ga mahukuntan kasar ta Zimbabwe su gaggauta daukar matakai don ceto tattalin arzikin kasar daga mummunan halin da ya shiga.

Gwamnatin Zimbabwe dai ta yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar zai bunkasa da kaso 2.7 % a wannan shekara, wanda kuma yayi hannun riga da hasashen da bankin duniya ya yi na kaso 1.5 %.