Kenya: Daya Daga Cikin Masallatai Mafi Jimawa Na Fuskantar Barazanar Rushewa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22286-kenya_daya_daga_cikin_masallatai_mafi_jimawa_na_fuskantar_barazanar_rushewa
daya daga cikin masallatan musulmi mafi dadewa da ke yankin Mawapa a kasar Kenya na fuskantar barazanar rushewa saboda rashin kula.
(last modified 2018-08-22T07:00:24+00:00 )
Jul 16, 2017 08:21 UTC
  • Kenya: Daya Daga Cikin Masallatai Mafi Jimawa Na Fuskantar Barazanar Rushewa

daya daga cikin masallatan musulmi mafi dadewa da ke yankin Mawapa a kasar Kenya na fuskantar barazanar rushewa saboda rashin kula.

Shafin yada labarai na standard media ya bayar da rahoton cewa, cibiyar kula da adana kayan tarihi ta kasar Kenya NMK ta sanar da cewa, wannan masallaci da aka gina tun shekaru 500 yana fuskantar barazana ta rushewa, saboda yadda aka bar shi ba tare da kula ba.

Bayanin cibiyar yace wurare irin wadannan masu matukar muhimmanci a tarihin kasar bai kamata mahkunta su sanya idi su lalace ba, domin kuwa irin wadannan wurare su ne kimarr kasar Kenya da tarihinta.

Babbar cibiyar kula da adana kayan tarihi a kasar Kenya dai ta saka wannan wuri a cikin muhimman wuraren tarihi na kasar wadanda suke da matsayi na musamman a tarihinta.

An gina wannan masallaci tun a cikin shekara ta 1500 miladiyya, kuma sakamakon rashin gyara da kulawa yadda ya kamata, ya sanya zafin rana da kuma ruwan sama, suna zaizaye ginin masallacin, wanda a cewar hukumar, zai iya rushewa matukar dai ba dauki mataki ba.