An Hallaka 'Yan Ta'adda Uku A Tsibirin Sina Na Kasar Masar
(last modified Sun, 16 Jul 2017 18:48:13 GMT )
Jul 16, 2017 18:48 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'adda Uku A Tsibirin Sina Na Kasar Masar

Sojojin kasar Masar Sun sanar da hallaka 'yan ta'adda uku a cibiyar tsibirin Sina

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Dakarun tsaron Masar cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan lahadi, Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda uku tare da cabke daya daga cikin su a tsibirin Sina na arewacin kasar.

Sanarwar ta ce farmakin da Sojoji ke kaiwa maboyar 'yan ta'adda na daga cikin ayyukan da suka sanya a gaba na tsarkake yankunan da 'yan ta'adda suke gudanar da ayyukansu na ta'addanci kuma a yayin kai wannan farmaki Sojojin sun rusa ma'ajiyar ababen fashewa da makamai na 'yan ta'addar guda biyar.

Gwamnatin kasar ta kara kaimi a yakin da ta keyi da kungiyoyin 'yan ta'adda masu alakar da kungiyar ISIS a tsibirin Sina, kasa da makunni biyu da suka gabata wani harin ta'addanci ya hallaka Sojojin Masar 21 a jihar Sina ta arewa, harin da kungiyar ISIS ta dauki alahakin kai sa.