Bam Ya Hallaka Wani Yaro A Bornon Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22298-bam_ya_hallaka_wani_yaro_a_bornon_najeriya
Wani yaro mai shekaru 10 ya rasa ransa a jihar Borno, da ke arewa maso gabashin Najeriya, bayan tarwatsewar damarar bam din da mayakan Boko haram suka daura masa.
(last modified 2018-08-22T07:00:24+00:00 )
Jul 16, 2017 14:19 UTC
  • Bam Ya Hallaka Wani Yaro A Bornon Najeriya

Wani yaro mai shekaru 10 ya rasa ransa a jihar Borno, da ke arewa maso gabashin Najeriya, bayan tarwatsewar damarar bam din da mayakan Boko haram suka daura masa.

Rundunar ‘yan sandan DSP  ta ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar jiya Asabar, wasu yara Fulani biyu Gambo Bukar mai shekaru 10 da kuma Umar bukar mai shekaru 8, daga kauyen Dalti da ke karamar hukumar Jere, suka fita kiwo, a nan ne suka gamu da wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, wadanda suka daura musu damarar bama baman, kafin sakinsu.

Rahoton ya kara da cewa, bayan dawowar yaran gida babu wanda ya bayyana abinda ya faru, wanda kuma garin cire damarar da aka daura musu, tarwatsewar bam din ya hallaka Gambo Bukar, yayinda shi kuma Umar aka garzaya da shi zuwa asibiti.