Dakarun tsaron Congo Sun Fatattaki 'Yan Tawaye Daga Yankin Kipese
Dakarun tsaron Jumhoriyar Demokaradiyar Congo na ci gaba da samun nasara na tsarkake yankin da 'yan tawaye suka mamaye a gabashin kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto kakakin Rundunar Sojin kasar Congo a jihar Kivo ta arewa a wannan Lahadi na cewa a fafatawar da Sojojin kasar ke yi da 'yan tawaye a yankin Kipese dake karkashin mamayar 'yan tawaye, Sojoji biyu ne suka rasa rayukansu yayin da a bangaren 'yan tawayen Mai Mai suka yi hasarar mayakan su guda biyar.
Rahoton ya ce har yanzu sojojin na ci gaba da fafatawa da 'yan tawayen a yankin na Kipese a kokarin da suke yi na kwato shi daga hanun su.
Cibiyar dake kula da hadin kan kabilun kasar ta Congo ta ce farmakin da Sojoji ke kaiwa 'yan tawayen gabashin kasar ya sanya fargaba da tsoro a zukatan fararen hula na yankin, wanda kuma hakan ya sanya suke gudun hijra daga yankin.