Sudan Ta Kudu: Zazzabin Cizon Sauro Ya Kashe Mutane 2000
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22324-sudan_ta_kudu_zazzabin_cizon_sauro_ya_kashe_mutane_2000
Hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta kudu ce ta sanar da wannan kididdigar ta mutuwar mutanen a cikin watanni shida.
(last modified 2018-08-22T11:30:24+00:00 )
Jul 17, 2017 11:56 UTC
  • Sudan Ta Kudu: Zazzabin Cizon Sauro Ya Kashe Mutane 2000

Hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta kudu ce ta sanar da wannan kididdigar ta mutuwar mutanen a cikin watanni shida.

Hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta kudu ce ta sanar da wannan kididdigar ta mutuwar mutanen a cikin watanni shida.

Bugu da kari hukumar agajin yi gargadi da jan kunne akan cewa cutar zazzabin cizon sauron za ta iya ci gaba da yaduwa a fadin kasar.

Dama a baya Majalisar Dinkin Duniyar ta sanar da cewa kaso 76% na mace-macen da ake yi a cikin kasar Sudan ta kudu na da alaka da ne da cutar izon sauro.

Wannan cutar na yaduwa ne adaidai lokacin da kasar ta Sudan ta kudu ta ke fada da yakin basasa a tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaban kasa Sivla Kiir da tsohon mataimakinsa Reikh Machar.