Harin Kunar Bakin Wake Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8 A Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22330-harin_kunar_bakin_wake_ya_yi_sanadiyyar_mutuwar_mutane_8_a_maiduguri
Majiyoyin tsaro a jahar Borno sun tabbatar da cewa, a yau wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a wani masallaci a lokacin sallar asubahia birnin Maiduguri fadar mulkin jahar ta Borno.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jul 17, 2017 13:02 UTC
  • Harin Kunar Bakin Wake Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8 A Maiduguri

Majiyoyin tsaro a jahar Borno sun tabbatar da cewa, a yau wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a wani masallaci a lokacin sallar asubahia birnin Maiduguri fadar mulkin jahar ta Borno.

Majiyoyin sun ce mutane 8 ne akalla aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sakamakon harin, yayin da wasu kimanin 15 suka jikkata.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana wanann sabon salo na Boko Haram na yin amfani da yara ko mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru da cewa lamari ne mai matukar hadari.

A cikin lokutan baya-bayan nan mayakan Boko Haram na yin amfani da wannan salo na yin amfani da mata ko kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake a Maiduguri, kamar yadda sukan yi hakan a sauran kasashen da ke fama da wannan matsala.