Najeriya : Malala Ta Gana Da 'Yan Matan Chibok
Matashiyar nan ta kasar Pakistan kuma 'yar rajin kare hakkin ilimin mata, Malala Yousafzai data ziyarci Najeriya ta gana da 'yan matan Chibok da aka ceto daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.
A yayin ganawa da 'yan matan a Abuja, Malala ta yi kira ga hukumomin Najeriya dasu samar da wani shirin ilimi na gaggawa a wannan kasa.
Bayan ganawa da mataimakin shugaban kasar, Ferfesa Yemi Osinbajo, Malala ta fadawa manema labarai cewa, gwamnatin Tarayya dana jihohi, yana da kyau su yi haddin gwiwa ta wannan fanni saboda mahimmancin da ilimin yake da shi ga samari da 'yan matan na Najeriya.
Wasu alkaluma da asusun kula da yara kanana na MDD cewa da Unicef, ya fitar sun nuna cewa sama da yara milyan goma a Najeriya basa zuwa makaranta, wanda kashi 60% daga cikinsu 'yan mata ne.
A farkon watan Yulin nan ne, Malala, 'yar shekara 20 a duniya ta kammala karantunta sakandare a birnin Birmingham na Burtaniya inda take da zama da iyalanta tun cikin shekara 2012 bayan mumunan harbin bindiga da mayakan Taliban suka mata a kasarta ta asali Pakistan.