Ma'aikatan NNPC na Najeriya sun janye yajin aiki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2236-ma'aikatan_nnpc_na_najeriya_sun_janye_yajin_aiki
Ma’aikatan kamfanin mai na NNPC a Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga sakamakon matakin da gwamnatin kasar ta dauka na karkasa kamfanin gida 7.
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 10, 2016 07:14 UTC
  • Ma'aikatan NNPC na Najeriya sun janye yajin aiki

Ma’aikatan kamfanin mai na NNPC a Najeriya sun janye yajin aikin da suka shiga sakamakon matakin da gwamnatin kasar ta dauka na karkasa kamfanin gida 7.

Rahotanni sun ce kungiyoyin gwadago na ma’aikatan sun aike da sakon gaggauwa ga mambobinsu da ke fadin kasar, inda suka umarce su da su koma bakin aiki.

Wannan na zuwa ne bayan da karamin ministan mai na kasar, Emmanuel Ibe Kachikwu ya gana da kungiyoyin yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.

A farko dai ma’aikatan sun koka kan yadda gwamnatin kasar ta yi gaban kanta wajen daukan matakin karkasa kamfanin ba tare da ta tuntube su ba, lamarin da ya tinzira su har suka tsindima cikin yajin aikin.

Gwamnatin dai ta ce ta dauki wannan matakin ne domin samar da sabbin sauye sauye a kamfanin na NNPC da nufin magance matsalar cin hanci da rahawa.

A cewar Alhaji Umar Dembo, tsohon ministan albarkatun mai a Najeriya ya ce, ya kamata a tuntubi ma’aikatan kafin gwamnati ta dauki wannan matakin na karkasa kamfanin.