Sojojin Burkina Faso Sun Fara Ficewa Daga Yankin Darfur Na Sudan
(last modified Thu, 20 Jul 2017 06:30:04 GMT )
Jul 20, 2017 06:30 UTC
  • Sojojin Burkina Faso Sun Fara Ficewa Daga Yankin Darfur Na Sudan

Ministan Tsaron Burkina Faso ya sanar da cewa sun fara janye Sojojin kasar dake aikin wanzar da zaman lafiya karkashin MDD a yankin Darfur na kasar Sudan

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, Ministan Harakokin tsaron kasar Burkina Faso Jean Claude Bouda ya bayyana cewa a daren talatar da ta gabata, tawagar farko na Sojoji kasar dake yankin Darfur na kasar Sudan sun sauka a birnin Ouagadougou babban birnin kasar, kuma zuwa ranar 23 ga wannan wata na yuli da muke ciki, za su kwashe Sojojin kasar gaba daya daga yankin na Darfur.

Rikicin yankin Darfur na kasar Sudan dai ya fara ne tun a shekarar 2003, bayan da kabilun yankin suka zarki Gwamnatin kasar da mayar da su saniyar ware a kasar, ya zuwa yanzu, rikicin ya lashe rayukan Mutane kimani dubu 300 tare da sanadiyar hijrar wasu kimanin miliyan biyu da rabi.

Ministan ya kara da cewa halin da kasar sa ke ciki a yanzu, a kwai bukatar karin yawan Dakarun tsaro domin tunkarar ayyukan ta'addanci da iyakokin kasar ke fuskanta.a cikin shekarun baya-bayan nan dai kasar ta Burkina Faso ta fuskanci hare-haren ta'addanci daga wasu kungiyoyi masu da'awar jihadi na kasar Mali.