Burkina Fasa Ta Janye Sojojinta Na Sulhu Daga Darfur Na Sudan
(last modified Thu, 20 Jul 2017 12:33:49 GMT )
Jul 20, 2017 12:33 UTC
  • Burkina Fasa Ta Janye Sojojinta Na Sulhu Daga Darfur Na Sudan

Ministar tsaron kasar Burkina Faso Jean Claude Bouda ne ya sanar da cewa tawagar farko ta sojojin sun isa birnin Ouagadougou a ranar talata.

Ministar tsaron kasar Burkina Faso Jean Claude Bouda ne ya sanar da cewa tawagar farko ta sojojin sun isa birnin Ouagadougou a ranar talata.

Claude Bouda ya ci gaba da cewa Sauran sojojin za su ci gaba da baro yankin Darfur na Sudan domin komawa gida daga nan zuwa 22 ga watan Yuli.

Ministan tsaron kasar ta Burkina Faso ya kuma kara da cewa; 'Yan sandan da kasar ta aika da su ne kadai za su ci gaba da zama a Darfur.

Burkina Faso ta janye sojojin nata ne saboda su koma gida su kalubalanci hare-haren ta'addancin da ake kai wa a cikin kasa.