Sojojin Masar Sun Hallaka Wasu 'Yan Ta'adda 30 A Yankin Sinai
(last modified Sat, 22 Jul 2017 05:47:46 GMT )
Jul 22, 2017 05:47 UTC
  • Sojojin Masar Sun Hallaka Wasu 'Yan Ta'adda 30 A Yankin Sinai

Rundunar sojin kasar Masar ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda alal akalla guda 30 a wani samame da suka kai musu a lardin Sinai da ke arewacin kasar.

Rundunar sojin Masar din ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma'a inda ta ce yayin wadannan hare-hare da suka kai, sun sami nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda da suka siffansu da cewa "masu tsananin hatsari" su 30 da kuma kama wasu guda biyar, sai dai ba su fadi sunayen wadanda aka kashe din ko kuma kungiyar da suka fito ba.

Haka nan yayin da yake karin bayani kan wannan labarin, kakakin sojin Masar din ya kara da cewa a yayin hare-haren dai sojojin sun gano wasu motoci 16 da aka makare su da bama-bamai inda tuni aka tarwatsa su.

Wasu rahotannin sun ce jiragen yakin sojojin Masar din sun kai hare-haren ne a maboyar 'yan ta'addan da ke garuruwan "Al-Uraish", "Sheikh Zawid" da kuma "Rafah" da ke lardin na Sinai.