Somaliya: An Rusa Wata Cibiyar al-Shabab A Kudancin Somaliya
Jul 22, 2017 07:39 UTC
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ce rundunar hadin gwiwa ta sojojin Somaliya da dakarun zaman lafiya na Afirka ne su ka kai harin a kusa da garin Tortoro a kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ce rundunar hadin gwiwa ta sojojin Somaliya da dakarun zaman lafiya na Afirka ne su ka kai harin a kusa da garin Tortoro a kudancin kasar.
A wani bayani da rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Afirka a Somalia ta fitar ta ce; Shakka babu rusa sansanin zai rage karfin da 'yan ta'addar su ke da shi wajen kai hare-hare akan al'ummar Somaliya.
Kungiyar ta'addanci ta al-shabab tana a matsayin babbar barazana ga tsaron Somalia da kuma sauran kasashen makwabta.
Tags