Masar: An Kashe 'Yan ta'adda 30 A Gundumar Sina Ta Arewa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22476-masar_an_kashe_'yan_ta'adda_30_a_gundumar_sina_ta_arewa
Sojojin Masar sun sanar da kashe 'yan ta'adda 30 a yankin Sina ta arewa a jiya juma'a.
(last modified 2018-08-22T07:00:26+00:00 )
Jul 22, 2017 07:44 UTC
  • Masar: An Kashe 'Yan ta'adda 30 A Gundumar Sina Ta Arewa

Sojojin Masar sun sanar da kashe 'yan ta'adda 30 a yankin Sina ta arewa a jiya juma'a.

Sojojin Masar sun sanar da kashe 'yan ta'adda 30 a yankin Sina ta arewa a jiya juma'a.

Jiragen yakin Masar sun kai hare-hare a sansanonin 'yan ta'adda da ke garuruwan "al-Arish' da "Sheikh Zuwaid" da kuma Rafah a gundumar Sina ta arewa.

Kakakin sojan Masar ya ce baya ga kashe 'yan ta'adda 30 an kuma lalata motoci 16.

Gundumar Sina ta arewa tana a matsayin babbar cibiyar 'yan ta'adda masu alaka da Da'esh.

A cikin shekarun bayan nan dai kasar ta Masar tana da fada da 'yan ta'addar da su ke tsananta kai hare-hare a cikin sannan daban-daban na kasar.