Gwamnatin Saudiyya Na Shirin Korar Dubban 'Yan Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22508-gwamnatin_saudiyya_na_shirin_korar_dubban_'yan_kasar_sudan
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta sanar da cewa, mahukuntan saudiyya sun sanar da su cewa za su taso keyar 'yan Sudan fiye da dubu 48 daga kasar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jul 23, 2017 06:47 UTC
  • Gwamnatin Saudiyya Na Shirin Korar Dubban 'Yan Kasar Sudan

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta sanar da cewa, mahukuntan saudiyya sun sanar da su cewa za su taso keyar 'yan Sudan fiye da dubu 48 daga kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, Karrar Tuhami babban darakta mai kula da harkokin 'yan Sudan mazauna kasashen ketare ya bayyana cewa, sun samu sako daga mahukuntan Saudiyya kan shirinsu na korar wasu dubban 'yan Sudan da ke zaune a kasar.

Ya ce yanzu haka sun fara shirin karbar wadannan mutane da za a taso keyar tasu daga Saudiyya, ya ce bisa ga doka kafin korar motane da suke zaune a kasa bisa ka'ida, a kan bayar da wa'adi na watanni uku domin su shirya, amma mahukuntan Saudiyya ba su bayar da irin wannan wa'adi ba.