Fadar Shugaban Najeriya Ta Wallafa Hoton Buhari
-
Buhari da wasu gwamnoni da kuma wasu jiga-jigan APC a birnin Landan. Hoto : Fadar shugaban kasa Najeriya
Fadar shugaban kasa a Najeriya, ta wallafa a shafinta na Twitter hoton shugaban kasar Muhammadu Buhari dake jinya a birnin Landan.
A watan Mayun daya gabata ne shugaba Buhari ya sake komawa birnin Landan domin yin jinya, saidai tun lokacin ne yau sama da wata biyu ba'a sake ganinsa ba a bainar jama'a.
Har yanzu dai ba'a bayyana hakikanin cutar dake damun Buhari mai shekara 74 ba.
A cewar fadar shugaban kasar, Buhari ya gana da wata tawa tawagar gwamnoni da wasu mukaraban jam'iyyarsa ta APC da yammacin jiya Lahadi.
Sanarwar da fadar shugaban ta wallafa a shaffinta na Twitter ta ce shugaban yana isar da kyakyawan fata ga dukkan 'yan kasar, kana kuma zai koma kasar da zarar likitocinsa sun bashi umurni.