ECOWAS Ta Yunkuri Anniyar Kayyade Iyali
Jul 24, 2017 01:16 UTC
Wakilan kasashe 15 na kungiyar ECOWAS / CEDEAO hadi da kasar Chadi da kuma Mauritania sun yunkuri anniyar rage yawan haihuwa da kusan rabi a cikin shekaru 13 masu zuwa.
Kasashen dai sun dau wannan matakin ne a wani taronsu na karshen makon jiya a birnin Ouagadugu.
A cewar Salifou Diallo shugaban majalisar dokokin Burkina Faso, kana wakilin kasar a kungiyar ta ECOWAS babban burin shirin shi ne karfafa yadda macce za ta haifi 'ya 'ya uku.
Matakin da kasashen suka dauka domin cimma wannan burin ya hada da cilastawa gwamnatocin kasashensu kara kashi 2% cikin kasafin kudin da suke warewa sha'anin kiwan lafiya a ko wacce shekara.
Tags