Najeriya: Akalla Mutane 8 Ne Su ka Mutu A Harin Maiduguri
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar tsaron Najeriya na cewa harin da aka kai da bom a jiya a sansanin 'yan gudun hijira a Maiduguri ya ci rayukan mutane 8 da jikkata wasu 11
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar tsaron Najeriya na cewa harin da aka kai da bom a jiya a sansanin 'yan gudun hijira a Maiduguri ya ci rayukan mutane 8 da jikkata wasu 11.
Birnin Maiduguri yana daga cikin wuraren da 'yan ta'adda su ka fi kai wa hare-haren, inda su ka fi amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake.
Shekaru 8 kenan a jere da kungiyar bokoharam ta kai hare-hare a cikin yankuna daban-daban na kasar, sai dai a cikin watannin bayan nan hare-haren sun takaita a jahar Borno.