Somaliya: Wasu 'Yan Kungiyar Al-Shabab Sun Mika Kawukansu Ga Hukuma
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22548-somaliya_wasu_'yan_kungiyar_al_shabab_sun_mika_kawukansu_ga_hukuma
Kamfanin dillancin labarun Xinuha na kasar Sin ya ce 'yan kungiyar a al-shabab da su ka mika kawukansu ga jami'an tsaro sun hada da kwamanda.
(last modified 2018-08-22T07:00:26+00:00 )
Jul 24, 2017 14:49 UTC
  • Somaliya: Wasu 'Yan Kungiyar Al-Shabab Sun Mika Kawukansu Ga Hukuma

Kamfanin dillancin labarun Xinuha na kasar Sin ya ce 'yan kungiyar a al-shabab da su ka mika kawukansu ga jami'an tsaro sun hada da kwamanda.

Kamfanin dillancin labarun Xinuha na kasar Sin ya ce 'yan kungiyar a al-shabab da su ka mika kawukansu ga jami'an tsaro sun hada da kwamanda.

Tun a baya, gwamnatin kasar ta Somaliya ta sanar da cewa tana maraba da duk  dan kungiyar ta al-shabab da ya mika kansa.

Tun a shekarar 2011 ne dai sojojin gwamnatin Somaliya da hadin guiwar dakarun tabbatar da zaman lafiya na Afirka su ka kori kungiyar daga cikin birnin Magadishu. Sai dai har yanzu  kungiyar tana rike da wasu yankuna kuma tana barazana ga kasashen makwabta da su ka hada da kasar Kenya.