Tarwatsewar Wata Mota Ta Yi Sanadiyyar Lashe Rayukan Mutane A Kasar Masar
Wata mota da aka makare da bama-bamai da tarwatse a kusa da wani wajen bincike a garin Arisha da ke arewacin lardin Sina ta Arewa na kasar Masar inda ta lashe rayukan mutane akalla bakwai.
Majiyar rundunar sojin Masar a jiya Litinin ta fitar da sanarwar cewa: Wani dan kunan bakin wake da ya makare motarsa da bama-bamai ya tarwatsa ta a kusa da wani wajen binciken ababan hawa a kudancin garin Arisha, inda ya yi sanadiyyar kashe mutane akalla bakwai dukkaninsu fararen hula.
Harin kunan bakin waken ya zo a daidai lokacin da jami'an tsaron Masar suke ci gaba da daukan tsauraran matakan tsaro a garin na Arisha da ma yankin Tsibirin Sina baki daya da nufin kawo karshen hare-haren wuce gona da irin a yankunan lardin.
Tun bayan da sojojin Masar suka kifar da zababbiyar gwamnatin Muhammad Morsi a ranar 3 ga watan Yulin shekara ta 2013 ayyukan ta'addanci suka kunno kai a kasar musamman a lardin Sina ta Arewa, inda ake kai hare-haren wuce gona da iri kan al'umma musamman kan jami'an tsaron kasar.