Shugaba Buhari Na Nigeria Ya Ce Komawarsa Gida Na Hannun Likitocinsa
Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Nigeria, wanda yaje jinya a kasar Britania ya bayyana cewa komawarsa gida na hannun likitocinsa, amma ya tabbatar da cewa yana samun sauki. Kuma zai dowa gida nan kusa ya koma bakin aiki.
Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto kakakin fadar shugaban kasa Mr Femi Adesina, yana fadar haka a yau Talata. Mr Adesina, ya kara da cewa shugaban ya bayyana haka ne a wata wasikar da ya rubuta wa shugaban kasar Guinea Alpa Conde, inda yake gode masa kan addu'oin da mutanen kasar Guinea a duk fadin kasar suka yi masa a cikin makon da ya gabata.
Mr Adesina ya ce kafin wannan wasikar shugaban ya zanta da tokwaransa na kasar Guinea Alpa Conde wanda ya kasance shugaban majalisar shuwagabannin kasashen Afrika na karba-karba. Shugaban ya koma kasar Britaniya ne tun ranar 7 ga watan Mayu domin ganin likotocinsa.