Majalisar Dokokin Zimbabwe Ta Bawa Mugabe Damar Zaben Manyan Alkalan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22590-majalisar_dokokin_zimbabwe_ta_bawa_mugabe_damar_zaben_manyan_alkalan_kasar
Majalisar dokokin kasar Zimbabwe ta bawa Shugaban kasar Robert Mugabe damar zaben manyan alkalan kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:27+00:00 )
Jul 26, 2017 01:56 UTC
  • Majalisar Dokokin Zimbabwe Ta Bawa Mugabe Damar Zaben Manyan Alkalan Kasar

Majalisar dokokin kasar Zimbabwe ta bawa Shugaban kasar Robert Mugabe damar zaben manyan alkalan kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a jiya Talata, majalisar dokin kasar zimbabwe ta yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima, wanda hakan zai bawa Shugaba Robert Mugabe damar nada manyan alkalan kasar.

Saidai a nata bangare, babbar jami'iyar adawar kasar ta bayyana cewa wannan mataki da majalisar dokokin kasar ta dauka, zai kawar da tsarin 'yanci da cibiyar tsaron kasar ke da shi.

Duk da irin kiraye-kirayen da kungiyoyin fararen hula na kasar suka yi na kadda 'yan majalisar su amince da wannan kudiri, jam'iyar Zanu mai milki a kasar ta yi amfani da yawan da take da shi cikin majalisar tare da kada kuri'ar amincewa.

Idan ba a manta ba da a shekarar 2013 ne aka yiwa kundin tsarin milkin kasar ta Zimbabwe gyara, wanda hakan ya ragewa Shugaban kasar karfin iko na nada Shugaban cibiyar shari'ar kasar da mataimakinsa gami da Shugaban kotun kolin kasar.