Najeriya : Buhari Ya Sake Ganawa Da Wasu Gwamnoni A Landan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22616-najeriya_buhari_ya_sake_ganawa_da_wasu_gwamnoni_a_landan
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake ganawa da wasu gwamnonin kasarsa a birnin landan inda yake ci gaba da karbar jinya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jul 26, 2017 13:54 UTC
  • Najeriya : Buhari Ya Sake Ganawa Da Wasu Gwamnoni A Landan

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake ganawa da wasu gwamnonin kasarsa a birnin landan inda yake ci gaba da karbar jinya.

Tawagar gwamnonin da suka gana da Buharin sun hada da na jihohin Kano, Borno, Benue, Akwa Ibom, Ebonyi da kuma Oyo. 

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da shugaban ya gana da wata tawagar gwamnoni uku da kuma wasu mukaraban jam'iyyarsa ta APC a ranar Lahadi data gabata, bayan da a karon farko ya gana da mataimakinsa Yemi Osinbajo a binin na Landan.

Har yanzu dai ba'a sanar da ainahin ciwan dake damun Buhari ba, aman fadar shugaban kasar ta ce yana murmurewa kuma nan bada jimawa ba zai koma gida, idan fa likitocinsa sun sallame shi. 

Buhari dan shekaru 74 ya kwashe fiye da wattani biyu yana jinya a birnin Landan lamarin da ya janyo kace-nace ba kadan ba a kasar.